Tambayoyin da a ke yawan yi

Tambayoyin da a ke yawan yi

Za a iya cire miki ita a yayin da wa’adinta ya cika(shekaru 5 ko 10) ,ko kuma lokacin da kike bukatar haihuwa

Ina , haka baza ta yiwu ba , don saida aka gwada ta matuka sosai.

Kada ki samu damuwa. Mata da yawa basa jin alamum wannan kirtanin, zaki iya neman agajin mai gida ta yiyu ya fiki dogayen yatsu,amma fa in kin damu, ki kokarta kiga liktarki.

Kada ki samu damuwa wani lokacin mahaifarki na yawo ne a yayin al’adarki, so a laokacin da ta yo kasa sai kiji ta kusa ta wajen gabanki, wani lokacin kuma yana nufin cewa IUD din ne da kanta ke kokarin fitowa , ki yi kokari ki ga masaniyar kiwon lafifa dan magance wannan matsalar, kada kice zaki taba ko ki cireta da kanki.

Akwai yiwuwar zuban jini ko dan digon jini ana sa miki ita .kuma wannan zuban jinin zai iya kaiwa har tsawon kwana uku ko wasu satuttuka yan kadan, ya danganci yadda jikinki ya karbi abin. Zaki iya rinka ganin digon jini bayan kwana biyu ko uku, wannan duk zaki daina ganinsu bayan wata uku.zaki iya amfani da disposable sanitary towel don tsaftace jikinki.

Lydia IUD bata hana daukan ciki nan gaba, ki tuna fa cewa komawa zakiyi kina haihuwa bayan an cire miki ita.

Ki lazumci analgesic yana da inganci wajan kawar da radadi.

Kada ki sami damuwa, ki sani cewa IUD copper zata sa al’adarki ta farko tazubar da jini sosai wanda bayan wata uku komai zai koma daidai. Idan bayan wata uku bata koma dai dai ba ki tabbatar da cewa kina ci sosai(wannan ba dole ne ya zama iri daya a tsakanin mata ba)

Bayan jinin al’adarki ko kuma bayan wata daya da sanya ta, sai ki sa dan yatsa ki ji ko zaki ji alamun kirtanin ta.

Lydia IUD tana fara aiki ne nan take bayan an sanya ta.

Matukar kin samu kwararriyar masaniyar kiwo lafiya ta sanya miki ita mai gida ba zai taba sanin cewa kina dauke da wani abu ba sai an fada masa. Kirtanin na da laushi sosai ta yanda ba zai taba yi masa lahani ba.

Lydia IUD bata bada kariya daga cutar kanjamau ko kuma su yi silar kamuwa da cutar. Don samun kariya daga wannan cutar muna baku shawarar amfani da kondom

Za ki iya jin dan radadi kadan a yayin da aka sanya miki ita . Mata dayawa na samun saukin radadin bayan sun dan huta kadan nayan mintuna. Za a iya shan analgesia idan radadi bai kau ba bayan awa 24(in kina zabi hakan )

Lydia bata yawo a cikin jiki ballantana taje zuciya ko kwakwalwa ko wani sashen jiki. Tana zama ne a cikin mahaifa kamar yadda kwallo ke zama a cikin bawonsa. Idan ma zai kauce ne daga mahaifa ne baya wuce tsakanin satayyan da aka sa shi. Wasu lokutan zaki iya rinka lura da ita dan ki tabbatar cewa tana inda take.

 

Kuna da wasu tambayoyin?

Ku turo mana da sako zamu amsa muka.

KU SADU DAMU

Ku gana da masanin kiwon lafiya a kan Lydia IUD

beLydiaSmart
close

Book Appointment

Get in touch with a health care provider.

We will get back to you as soon as possible on the health provider’s availability.

Don neman Karin bayani gameda hanyoyin bada tazarar haihuwa
ku kai ziyara ga wannan shafin yanargizo www.honeyandbanana.com