Da farko dai idan kina son sa Lydia IUD, ki samu masanin kiwon lafiya ki labarta mata. Sai ta duba ta gano shin ko ta dace dake ko kuma a’a. A sani cewa fa Kwarararriyayar masanin kiwon lafiya ce ke sa ko cire Lydia IUD.
Za a iya sa miki ita a kowane lokaci amma masu kiwon lafiya sun fi son a sa ta a lokacin al’ada. Za ki iya sata a kowane lokaci matukar baki da juna biyu.
Lydia IUD na fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba in an sanya ta a mahaifa. Bayan an sata zaki cigaba da harkokinki nayau da kulllum har ma da kwanciyar aure da mai gida.
Ki rinka yin amfani da yatsanki don jin alamun wannan kirtanin lokaci bayan lokaci musamman ma a lokacin al’adarki, wannan zai taimaka miki wajan tabbatar da cewa Lydia IUD bata bar mazaunin taba. Kada ki ja wannan kirtanin ko ma ki yi yunkurin cireta da kanki.
Wasu matan zasu rinka jin takurar jijiya, yawan zuban jinin al’ada, ko kuma wargazazziyar al’ada. Kada ki damu wannan duka a tsakanin yan satuttuka zasu baje zaki nemesu ki rasa. Amma idan hakan ta dore har na tsawon wata uku, to ki maza ki ga likitarki don a samu a shawo kan matsalar nan.
Za a iya cire Lydia IUD tun kafin wa’adinta su cika idan kina son samun wani cikin ko kuma don wani dalili da ke iya afkuwa.
Don neman Karin bayani gameda hanyoyin bada tazarar haihuwa
ku kai ziyara ga wannan shafin yanargizo
www.honeyandbanana.com