Lydia na da inganci sosai,ga araha kuma mafi kyawun hanyar bada tazarar haihuwa. Wasu mutanen nace mata Lydia coil. Tana dadewa sosai(har tsawon shekaru 10) kuma bata dauke da wata kwaya mai gurbata jiki. Bugu da kari ma, mata masu amfani da Lydia IUD zasu koma haihuwa bayan an cire musu ita.ba tareda bata lokaci ba.
Koma bayan cewa ana anfani da Lydia IUD wajen bada tazarar haihuwa tsakanin yara , kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato W.H.O ta tabbatar da cewa ita wannan IUD din itace mafi ingattaciyar hanyar bada tazarar haihuwa na gaggawa mai inganci(tafi kwayoyi inganci) in an sanya ta bayan saduwa da abinda bai wuce kwanuka 5 ba.
Lydia IUD wata yar karamar robace wacce aka lullube da karfen copper, tana zuwa kan samfuri daban daban , kusan samfura 5 amma wacca tafi fice a cikinsu itace mai samfurin T, wacce aka fi sani da Copper T. don amfani da Lydia wajen bada tazarar haihuwa, sai a sami likita, ko masanin kiwon lafiya ya sa miki ita. Matukar tana cikin mahaifa Lydia zata hana maniyyin da’ namiji kusantar mahaifarki kinga ba batun daukan ciki kenan.(shi wannnan maniyyin da aka hana shi tafiya shine yake sanadiyyan shigar ciki)
Lydia bata hana saduwar aure tsakanin ma’aurata,saboda haka ba sai an yi wasu yan kimtse kimtse ba kafin ki sadu da mai gida. Ba yawan dube dube. A duk lokacin da kike bukatar mai gida, ga fili ga maidoki.
Zaki iya dogara da Lydia IUD wajen bada tazarar haihuwa har na tsawon shekaru 10 matukar kina dauke da ita.
Lydia IUD na da matukar saukin samu ga mafiya yawan mata kuma yana jimawa yana aiki har na tsawon shekaru 10, ki duba kiga da a ce zaki rinka sayan kwayoyi ne har na tsawon shekaru 10 nawa zaki kashe.
Ana cire miki shi zaki koma kina haihuwa nan take, wanna gaskiya ne, tunda baya ta’ammali da kwayoyin jiki kinga ba sai kin jira wani lokaci mai tsawo ba kafin ki fara haihuwa.
Lydia IUD bata dauke da kwayoyin gurbata jiki , akan haka ba zancen ramewa ko na kara nauyi(ko da wasa) ko ma ku rinka jin jiri da sauransu ko kuma ma ya tsayar miki da al’adarki. Ba wannan zancen. Ko kinsan cewa masu shayarwa ma zasu iya amfani da ita bayan haihuwa ba tareda ya rage yawan ruwan nononsu ba? Haka ma mata masu ciwon suga ko masu kiba zasu iya amfani da IUD.
Mata masu dauke da Lydia IUD na more rayuwar saduwa da iyalansu, suna samun cin burinsu na karatu da wajen ayukansu kuma zasu iya komawa suna haihuwa, zasu raini yaransu kuma su kula da iyalansu cikin sauki ba tareda gumin goshi ba. lydia ta dace da kowace irin mace wacce ta taba haihuwa ko kuma wadanda suka gama haifan iya yaran da suke so a duniya.
Ba wanda zai iya sanin cewa kina dauke da Lydia IUD saboda ba wanda zai iya ganinta a cikin mahaifarki.
Don neman Karin bayani gameda hanyoyin bada tazarar haihuwa
ku kai ziyara ga wannan shafin yanargizo
www.honeyandbanana.com